Shekaru 3 ke nan bayan barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19 a duniya. A cikin wadannan shekaru 3 da suka gabata, ko da yaushe kasar Sin tana mayar da jama’arta da rayukansu a gaban komai. Ta kyautata matakan yaki da cutar bisa lokaci da yanayin da ake ciki, da daidaita aikin raya tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasa, da na dakile yaduwar cutar yadda ya kamata. Lamarin da ya sa aka magance yaduwar nau’o’in kwayoyin cutar masu haddasa saurin mutuwa a kasar, tare da kiyaye rayuka da lafiyar jama’arta yadda ya kamata.
Ahmad Adamu Umar, dan Najeriya ne wanda aka fi sani da Khalifa Ado Namagaji Kazaure, a yanzu haka yana karatun digiri na biyu a fannin tsaron yanar gizo ta Intanet a jami’ar kimiyya da fasahohin laturoni ko kuma UESTC a takaice dake birnin Chengdu na lardin Sichuan na kasar Sin. A hirar da ya yi da Murtala Zhang, Malam Ahmad ya bayyana dalilin da ya sa ya kudiri aniyar zurfafa karatu a kasar Sin, da yadda za’a iya inganta hadin-gwiwa da mu’amala tsakanin Najeriya da kasar Sin......
A bana ne ake cika shekaru 20, da Amurka da kawayenta suka kaddamar da yaki a kasar Iraki, ba tare da samun izini daga MMD ba, bisa hujjar cewa, ta gano makaman kare-dangi a kasar ta Iraki. Amma daga baya, an tabbatar da cewa, Iraki ba ta da irin wadannan makamai. Wannan ya kara tabbatar da zalunci da nuna fin karfi da Amurka ke nunawa kan wasu kasashe.
Cristiano Ronaldo ya buga wa Portugal wasa na 197, ya kuma ci kwallo biyu a wasan neman shiga Euro 2024, bayan doke Liechtensen 4-0.Mai shekara 38, shine kan gaba a yawan cin kwallaye a tawaga a tarihi mai 120 kawo yanzu.
A yayin babban taron tattaunawa tsakanin Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da jam'iyyun siyasa na duniya da aka gudanar ta kafar internet a kwanakin baya, shugaban kasar Sin Xi jinping ya gabatar da shawarar wayewar kai ta duniya. A cikin shirinmu na yau za mu saurari ra'ayin wani shahararren shehun malami dan kasar Mali dangane da wannan shawara, gami da rawar da jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ke takawa a duniya.